No Image Available

RISALA ZUWA GA MUSULMI

 Author: Prof. Sani Abubakar Lugga  Publisher: Lugga Press
 Description:

Akwai dalillai guda biyu da suka sa aka rubuta wannan Wasiqa mai taken “Risala” zuwa ga ‘Yan Uwa Musulmi. Dalili na farko shi ne, Qyama da Tsangwama da ake yi ma Musulmi waxanda suka sanya Majalisar Xunkin Duniya ta sanya Ranar 15 ga Watan Maris na ko wacce Shekara Miladiyya ta zamo Ranar Kawad Da Qyamar Musulmi Ta Duniya. Wasiqar ta yi bayanin cewa ana ta vavatun cewa wai Musulmi su ne ‘Yan Ta’adda kuma wai Musulunci Ta’addanci ne; SubhanalLah! Wasiqar ta yi kira mai qarfi da babbar murya a kan Musulmi su tashi tsaye su nuna kuma su tabbatar ma Duniya cewa Musulunci shi ne lafiya da zama lafiya da ci gaban Jama’ar Duniya. Wannan Risala ta yi bayanai gamsassu da suka tabbatar da cewa Musulmi sun yi qage-qage na Kimiyya da Fasaha da Sana’a. Misali, Musulmi ne suka qago Harsashi na Bindiga, su suka yi jagoranci wajen Ayyukan Likitanci da na Magunguna, kuma su suka inganta Ayyukan Gona. Amma yanzu duk an bar Musulmi a baya domin suna dogaro wajen ci gaban da waxanda ba Musulmi ba ke tafiyarwa wajen waxannan muhimman ayyuka da Musulmi tun farko suka asssasa amma yanzu suka watsar!

Dalili na biyu shi ne, jawo hankali zuwa tavarvarewar halayen Mutane gaba xaya. Risalan nan ta bayyana cewa a yau, Qasashe da yawa na Duniya suna cike da Shugabannin Siyasa Azzalumai, Ma’aikata Lalatattu, Shugabannin Addini da na Gargajiya Marassa Mutunci, Alqalai da Ma’aikatan Tsaro Maciya Hanci, Matasa ‘Yan Kwaya da Mashaya Giya, Talakawa Marassa Amana; da dai sauran munanan halaye na Jama’a. Waxannan miyagun halaye suka sanya tashin hankula, kashe-kashe, da ta’addanci suka addabi Duniya. Ko da yake an rubuta wannan Risala musamman zuwa ga Al-Ummar Musulmi, ya kamata waxanda ba Musulmi ba su amshi wannan Risala da zuciya guda kuma su fahimci Musulmi da Musulunci domin haxin kawuna, da gyaran hankula da xabi’u da aqidu sabo da a cimma lafiya, da zaman lafiya da qaruwar arziki a ko ina a Duniya. Wanna shi ne tafarki madaidaici wanda kowa da kowa ke muradin samun irin shi.

Other Books From -

No Image Available Fadakarwa A Kan RENON YARA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available RE-BRANDING NIGERIA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available HIJRAH TO NEGAS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available NATURAL DISASTERS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available JNI AT 50 Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available LE KANEM-BORNOU A PREMIERE VUE Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available ISLAMISE AND CHRISTIANISE NIGERIA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available HATTARA MA’AURATA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available A GLOSSARY OF MANAGEMENT TERMS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available GAWURTACCEN LARDI Prof. Sani Abubakar Lugga

Other Books By - Prof. Sani Abubakar Lugga

 Back