No Image Available

GAWURTACCEN LARDI

 Author: Prof. Sani Abubakar Lugga  Publisher: Lugga Press
 Description:

Wannan Littafi ya qunshi Taqaitaccen Tarihin Qasashen Katsina Da Daura, watau tsohon Lardin Katsina wanda a yanzu ya zama Jihar Katsina tun daga wajejen shekarar 991 zuwa 2022 Miladiyya. Tarihin ya kama tun kamin zuwan Musulunci a Qasar Hausa, da lokacin shigar Musulunci har ya zuwa lokacin Mulkin Mallaka na Turawan Ingilishi da Mulkin Siyasa da Mulkin Sojoji. Gawurtar Lardin Katsina ta fito fili lokacin da Kolejin Farko a Jihar Arewa ta yaye Shugabannin Farko; kamar su Shugaban Najeriya na farko Alhaji Abubakar Tafawa Valewa, Pirimiyan Jihar Arewa Sardaunan Sokoto Alhaji Ahmadu Bello, Gwamnan Jihar Arewa Wazirin Barno Alhaji Kashim Ibrahim, Minister Makaman Bida Alhaji Aliyu, Minister Wazirin Katsina Alhaji Isa Kaita, da sauransu. Kamar yadda za’a gani a cikin wannan Littafi, waxannan Mashahuran Mutane sun fara haxuwa ne a Katsina lokacin karatunsu a zamanin Babansu Sarki Muhammadu Dikko da Abokinsu Sarki Usman Nagogo.

Bayan haka, wannan Gawurtaccen Lardi ya fi kowane ci gaba a duk faxin Najeriya ta Arewa, kamar yadda za’a iya gani a cikin wannan Littafi. Misali, a wannan Lardi ne aka fara gina Fadar Sarauta shekaru 1,200 da suka wuce; a nan ne aka fara gina Jami’ar Musulunci a shekarar 1493 Miladiyya; a nan ne aka fara gina Kolejin Zamani a shekarar 1921. Kuma Sarkin Zamani da ya fara zuwa Makka da Ingila, da Dan Najeriya da ya fara zuwa Makka a cikin Mota, da Lauyoyin farko da Injiniyan farko, da Janar na Soja Bahaushe na farko, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Bahaushe na farko, da Mai Aikin Rediyo na farko, da Likitan Dabbobi na farko, da Ministan Tarayyar Najeriya na farko a zamain Turawa da Makarantar Haxa Magunguna ta farko, da Cibiyar Binciken Aikin Gona ta farko, da dai sauransu, duk wannan Lardin ne ya fara samar da su a Najeriya ta Arewa!

Other Books From -

No Image Available Fadakarwa A Kan RENON YARA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available RE-BRANDING NIGERIA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available HIJRAH TO NEGAS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available NATURAL DISASTERS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available JNI AT 50 Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available LE KANEM-BORNOU A PREMIERE VUE Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available ISLAMISE AND CHRISTIANISE NIGERIA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available HATTARA MA’AURATA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available A GLOSSARY OF MANAGEMENT TERMS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available GAWURTACCEN LARDI Prof. Sani Abubakar Lugga

Other Books By - Prof. Sani Abubakar Lugga

 Back