No Image Available

YI MA KAN KA HISABI KAMIN ALLAH YA YI MAKA

 Author: Prof. Sani Abubakar Lugga  Publisher: Lugga Press
 Description:

Lokacin da Allah (SWT) Ya nufe ni da jagorancin kafa Jami’ar Musulunci ta farko a Najeriya a Katsina a shekarar 2005 Miladiyya (Al-Qalam University, Katsina), sai na riqa koyar da Kamalallen Darasi (watau General Studies) wanda ya shafi rayuwar Musulmi ta yau-da-kullum ga xalibai kimanin 1,200, daga samari har zuwa magidanta; maza da mata. A lokacin ne na lura da cewa akwai abubuwa da dama da ke bukatar ilmantarwa. Daxin daxawa, a matsayi na na Wazirin Katsina, sai na lura da tsananin jahilcin mutane a kan rashin ilmin rayuwar yau-da-kullum daga irin koke-koken da jama’a ke gabatarwa a Majalisar Mai Martaba Sakin Katsina. Don haka, daga shekarar 2007 Miladiyya, sai na fara rubuta bayanan muhimman abubuwan rayuwa da na fahimci sun fi neman ilmantarwa da harshen Turanci domin da harshen ne nake koyarwa a Jami’ar Katsina. Amma daga baya sai na ga ya fi dacewa in fassara abubuwan da na tanada cikin harshen Hausa domin Jama’ar mu zasu fi amfana da su. Alhamdu lil Lah, wannan shi ne Littafin a kan wannan aiki. Allah Ya sa mu dace, domin Shi kaxai ne Masani, ameen.

An ruwaito cewa, Khalifa Umar bin Khattab (RLA) ya ce:- “Ka yi ma kan ka Hisabi (a Duniya), kamin Allah (SWT) Ya yi maka Hisabi (a Lahira)”. Wannan Littafi ya jingina ne da wannnan umurni na Sayyidina Umar (RLA). Duk Musulmi ya kamata kullum kamin ya kwanta barci, ya tambayi kan shi, “me da me na yi a yau na ibada da na mu’amalla?” Idan ya sanya abubuwan da ya yi a bisa mizani, to, sai ya dubi abubuwan halal da ya yi, ya yi ma Allah godiya a kan su; kuma ya dubi abubuwan haram da ya yi, ya yi ma Allah istigfari a kan su da niyyar ba zai qara yin su ba. Daga nan sai ya duba abubuwan da ya yi na zalunci tsakanin shi da mutane, sai ya yi niyyar gyarawa ya kuma nemi gafarar waxanda ya yi ma zaluncin. A taqaice, an wallafa wannan Littafi musamman domin taimaka ma Musulmi wajen fahimtar mas’alolin rayuwa na yau da kullum da yadda Musulunci ya bayyana hanyoyin yi ma kai Hisabi da kuma warware taqaddamar da zata iya shiga tsakanin Musulmi. Wannan zai ba Musulmi damar yin sulhu tsakanin su cikin sauqi ba tare da zuwa ofisoshin‘Yan-Sanda ko Kotunan Alqalai ba. Kuma zumunci, lafiya da zama lafiya da qaruwar arziki za su yalwata.

Other Books From -

No Image Available Fadakarwa A Kan RENON YARA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available RE-BRANDING NIGERIA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available HIJRAH TO NEGAS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available NATURAL DISASTERS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available JNI AT 50 Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available LE KANEM-BORNOU A PREMIERE VUE Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available ISLAMISE AND CHRISTIANISE NIGERIA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available HATTARA MA’AURATA Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available A GLOSSARY OF MANAGEMENT TERMS Prof. Sani Abubakar Lugga
No Image Available GAWURTACCEN LARDI Prof. Sani Abubakar Lugga

Other Books By - Prof. Sani Abubakar Lugga

 Back