Hattara Maaurata

Lokacin da Allah (SWT) Ya nufe mu da kafa Jami’ar Musulunci ta farko a Najeriya a Katsina a shekarar 2005 miladiyya, sai na riqa koyar da Darasin “General Studies” wanda ya shafi rayuwar Musulmi ta yau-da-kullum ga xalibai kimanin 1,200, daga samari har zuwa magidanta. Kuma tun daga 2002 na ke sauraren irin koke-koken da jama’a ke gabatarwa a Majalisar Mai Martaba Sakin Katsina. A waxannan wurare biyu ne na lura da tsananin rashin ilmin mutane a kan rayuwar yau-da-kullum. Don haka, na wallafa Littafi mai suna “Yi Ma Kan Ka Hisabi” a 2016 mai xauke da bayanan muhimman abubuwan rayuwa da na fahimci sun fi neman ilmantarwa. Domin wancan Littafin yana da girma kwarai, sai na tsakuro abin da ya shafi aure daga cikin sa, na yi wasu qare-qare da gyare-gyare na wallafa wannan qaramin Littafin. Allah Ya sa mu dace, domin Shi kaxai ne Masani, ameen. Bissalam. Na ku, Wazirin Katsina.

Close Menu