Gawurtaccen Lardi

Wannan Littafi ya qunshi tarihin Qasashen Katsina Da Daura, watau  tsohon Lardin Katsina wanda a yanzu ya zama Jihar Katsina tun daga shekarar 991 zuwa 2016 miladiyya; watau shekaru 1,025 da suka wuce. Tarihin ya kama tun kamin zuwan Musulunci a qasar Hausa, da lokacin shigar Musulunci har ya zuwa Mulkin Mallaka na Turawan Ingilishi da Mulkin Siyasa da na Sojoji. Ba shakka, wannan Gawurtaccen Lardi ne ya fi ko wane ci gaba a duk faxin Najeriya ta Arewa, kuma za’a iya ganin haka idan aka karanta ire-iren tsare-tsare da ayyukan raya qasa da aka aiwatar a duk sassan Lardin kamar yadda suke qunshe a cikin wannan Littafi. A wannan Lardi ne aka fara gina Fadar Sarauta fiye da shekaru 1,000 da suka wuce, a nan ne aka fara gina Cibiyar Musulunci a shekarar 1493 miladiyya, a nan ne aka fara gina Kolejin Zamani a shekarar 1921. Lauyoyin farko da Injiniyan farko, da Janar Bahaushe na farko, da mai Aikin Rediyo na farko, da Likitan Dabbobi na farko, da Ministan Tarayya na farko da Makarantar Haxa Magunguna ta farko, da Cibiyar Binciken Aikin Gona ta farko, da dai sauransu, duk wannan Lardin ne ya fara samar da su a Najeriya ta Arewa!l

Close Menu